AREWATOPLOADED.COM

YOUR CHOICE THE BEST OF ALL.....

you are welcome to arewatoploaded You are welcome to arewatoploaded

Friday, August 3, 2018

Kaka Ta Sayar Da Jikarta Kan Kudi Naira Dubu 200

Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom sun cika hannu da wata mata mai shekaru 37 mai suna Ekaette Obot bisa zargin sayar da jikarta kan naira dubu dari biyu.

A yayin da ake gurfanar da ita gaban manema labarai, Misis Obot ta bayyana cewa ta yanke hukuncin sayar da jaririyar ne domin saukewa ‘yarta mai shekaru 18 mai suna Blessing Okon nauyin reno kasancewar ba su da karfi.
#Rariya


Kakar ta kara da cewa a matsayinta na mai aikin goge-goge ba ta da karfin da za ta iya ciyar da ‘yarta, jikarta da kuma ita kanta don haka ta yanke shawarar sayar da jikar tata.

No comments:

Post a Comment