Taron rabon kudin wanda aka gudanar da shi a fadar gwamnatin jihar, dukkan wadanda suka ci gajiyar kudin ‘yan mata ne masu matsakacin shekaru.
Rabon kudin yana daga cikin kudirin raba naira milyan bakwai ga ‘yan matan jihar da mai baiwa Gwamnan Kebbi shawara kan harkokin siyasa da wutar lantarki, Yusuf Gwandu yake yi, inda a karon farko aka baiwa mata dari kafin daga bisani a dora daga inda aka tsaya.
A yayin da take gabatar da jawabi, Uwargidan Gwamnan ta ja hankulan ‘yan matan da suka amfana da kudin da su yi amfani da shi ta hanyoyin da suka dace domin ganin sun amfana da tallafin da aka ba su.
Wata daga cikin wadanda suka ci gajiyar kudin, ta bayyana cewa tunda aka haife ta ba ta taba rike koda dubu biyar da sunan siyasa ba, sai a dalilin matar Gwamnan Kebbi Dakta Zainab Bagudu, don haka suna yi mata fatan Allah ya saka mata da alkairi.
Shi ma a nashi bangaren, Yusuf Gwandu bayan ya jawo hankulan ‘yan matan da suka ci gajiyar kudin, ya kuma kara da cewa ba komai ya jawo hankalinsa da bada tallafin ba, illai yadda ya ga Uwargidan gwamnan tana fadi-tashi wajen tallafawa mata musamman don ganin sun dagora da kansu.
#Rariya

No comments:
Post a Comment