Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a ranar Alhamis din da ta gabata ya bayyana cewa, wadanda ke lalata kasar nan ba bu lallai su kasance mamugunta sai dai zababbun shugabanni masu rike da madafun iko da suka zuba idanu tare da yin shiru kan al’amurran da suka shafi kasar.
Obasanjo ya bayyana ire-iren wadannan mutane a matsayin makiya kasar nan ta Najeriya, inda ya sha alwashin ba zai rike bakin sa yayi shiru yayin da munanan al’amurra ke faruwa ba,
sai dai ya ce a shirye yake ya goyi bayan duk wanda zai kai kasar nan ga gaci.
sai dai ya ce a shirye yake ya goyi bayan duk wanda zai kai kasar nan ga gaci.
Dattijon na kasa ya yi wannan jawabi tare da kaddamar da matsayar sa yayin da tsohon ministan ayyuka na musamman,Kabiru Tanimu Turaki, ya ziyarce shi a gidan sa dake babban birnin Abeokuta a jihar Ogun.
Kamar yadda shafin jaridar TheNation ya bayyana, Turaki ya kai ziyara ne birnin Abeokuta domin bude sabon shafi tare da neman aminci da tabarraki na Obasanjo dangane da kudirin sa na neman takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019.
Obasanjo ya fahimci cewa, kasar Najeriya na da albarkar amintattun mutane nagari da ka iya jagoranci ko ina a fadin duniya, inda ya bayyana cewa ba zai gaza ba wajen fafutikar sa taneman tsayayyen jagora da zai kai ta ga gaci.
#Rariya

No comments:
Post a Comment