…wani koraren Ko’odineta ne ya jagoranci kona jar hula a Jigawa, cewarsu
Kungiyar magoya bayan Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso dake jihar Jigawa sun bayyana cewa suna nan tare da jagoran su, inda suka tabbatar da cewa duk inda ya sa gaba ko ya sa kafar sa nan za su bi.
Jagoran Kwankwaaiyya na jihar, Shehu M. Bello (Shehun Garu) shi ya tabbatar da hakan. Inda ya kara da cewa wanda ya tara yara kanana da ba su san ciwon kansu ba suka kona jar hula a Jigawa tuntuni an jima da korarsa daga Kwankwasiyya.
Shehun Garu ya ci gaba da cewa yanzu Kwankwasiyya ta zama babbar barazana ga jam’iyyar APC reshen jihar Jigawa, wanda hakan ya sanya zaben 2019 na wanda ya iya allonsa ne.
Jigon Kwankwaaiyyan ya kara da cewa a shekarar 2015 ‘yan Kwankwasiyya sun yi matukar taka rawar gani a nasarar da APC ta yi, don haka ficewar Sanata Kwankwaso da magoya bayan sa daga APC ya zama babbar barazana ga APC a jihar Jigawa da ma kasa baki daya.
#Rariya

No comments:
Post a Comment