AREWATOPLOADED.COM

YOUR CHOICE THE BEST OF ALL.....

you are welcome to arewatoploaded You are welcome to arewatoploaded

Saturday, August 4, 2018

Koriya ta Arewa ta ci gaba da shirinta na nukiliya


Makamin Nukiliyar Koriya ta Arewa
Image captionRahoton ya zargi Koriya ta Arewa da yin watsi da takunkumin da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniyar ya kakaba ma ta kan hakan

Wani sabon rahoto da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya gabatar, ya nun Koriya ta Arewa ba ta daina shirinta na kera makaman nukiliya ba, ta kuma yi biris da takunkuman da aka kakaba mata tare da saida wa wasu kasashe makamai.
Rahoton wanda kwararru suka gudanar da bincike akai sun ce abin da Koriya ta Arewa ta yi ya tabbatar da sabon takunkumin Majalisar Dinkin Duniya akan ta.
Har wa yau rahoton ya ce Arewar na hada-hadar cinikin makamai ga masu fasakwabrinsa da suke sayar wa ga sojin Syria, da kananan makaman a Libya da Yemen da Sudan.
Sai dai jami'an Diflomasiyyar Koriya ta Arewar ba su ce uffan kan rahoton ba, da zarge-zargen da akai mu su.

No comments:

Post a Comment