AREWATOPLOADED.COM

YOUR CHOICE THE BEST OF ALL.....

you are welcome to arewatoploaded You are welcome to arewatoploaded

Friday, August 3, 2018

Hajjin Bana:Ana Kan Jigilar Maniyyata Aikin Hajji A Najeriya

Biyo bayan fara jigilar maniyyata aikin Hajjin bana (2018) da hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta kaddamar ranar 21 ga watan Yuli a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe dake birnin tarayya Abuja, zuwa yanzu an kwashi maniyyata daya bisa uku na adadin Alhazan dake Nijeriya.
Jiragen kamfanonin Maxair, Medview, da Flynass ne suke jigilar Alhazan, kuma har zuwa yau dinnan ba’a samu ko wace irin matsala daga garesu ba, Wanda wannan ba karamar nasara bace, in ka duba baya ka tuna irin yadda kamfanonin jirage suke cin Karen su babu babbaka, wanda wannan canji da aka samu abun a yabawa Hukumar ce.
Barista Abdullahi Mukhtar Muhammad, shine shugaban Hukumar Alhazan Naijeriya (NAHCON), kuma a lokacin jagorancin sa ne ya kawo tsari da doka da oda a Hukumar Alhazan. A baya Alhajin Naijeriya baisan wani dadi daga Hukumar Alhazai ba, in ka duba a baya yadda ake zubar da mutane a filayen jiragen sama na jiddah suyi kwanaki suna kwana cikin sanyi ba tare da sun San ranar da za’a kwashe su ba, da dai sauran wahalhalu kala kala.
A wannan lokaci Mukhtar ya tsara yadda za’a kamawa Alhazai masaukai a kusa da Haramin makkah, za’a baiwa Alhaji Abincin Karin kumallo, sannan za’a bashi abincin Dare, haka abun yake a filin Arfa da Mina.
A birnin Madina kuma manyan Masaukai (HOTEL) irin su Tayba wadanda suke kewaye da Haramin Madina su Hukumar Alhazai ta kamawa Alhazan Naijeriya, wadanda duk manyan masu kudi da manyan kasashe masu arziki ke kamawa. Kazalika nanma ga abincin karin kumallo dana Dare.


Sannan ta bangaren zirga zirga kuma, a yanzu kasar Naijeriya ta shiga sahun kasashen da suke daukan manyan Bus ta zamani, wanda ke dauke na’urar sanyaya mota, ga bandaki a ciki, sannan da wurin igiyar chajin Waya, duk anyi wannan ne dan jin dadin Alhaji.
A baya haka kawai wasu dillalai zasuje Saudi suyi zaman dirshan ana hada baki da wasu makiya Allah, ana karban kudade da sunan kama masaukai masu nagarta, sai su kama wulakantattu suna saka sauran kudaden a Aljihunsu, zuwan Barista Mukhtar duk ya zakulo irin wadannan zalunci ya fatattake su, wannan shine dalilin da yasa wasu suka dinga yakarsa da kalamai da sauran miyagun maganganu wadanda a karshe suka fadi ba Nauyi.
Na san wani zai yi tambayar cewa ai a lokancin sa kujerar Makkah ta yi tsada. Wanda wannan tsadar ba iya kan kujerar Hajji ta tsaya ba, hatta cikin kasuwanni ta shiga ta daga farashin kayayyakin masarufi, saboda tashin da dala tayi a lokacin zuwan sabuwar gwamnatin shugaba Buhari wanda har zuwa yau dinnan dala tana nan a inda take.
A karshe ina yabawa shugaban Hukumar Alhazai ta kasa, Barista Abdullahi Mukhtar Muhammad, bisa jajircewa da yayi ya kuma toshe kunnuwansa domin ya kawo gyara, ya kuma fatattaki cin hanci da rashawa a ma’aikatar. Wanda da Ace shugaba Buhari yasan ba gaskiya yakeyi ba, na tabbata da tuni ya cikawa rigarsa iska.
Muna addu’a Allah ya karbi ayyukan Hajji na duk wani musulmin da ya samu zuwa dan gabatar da aikin Hajji, wanda za’a gabatar a wannan wata mai albarka, ya kawo mana jagorori masu gaskiya da rikon amana wadanda zasuci gaba da jan ragamar ma’aikatu, da sauran jagorori na siyasa.

#Rariya

No comments:

Post a Comment