AREWATOPLOADED.COM

YOUR CHOICE THE BEST OF ALL.....

you are welcome to arewatoploaded You are welcome to arewatoploaded

Saturday, July 28, 2018

Dalilin Da Ya Sa Ban Koma Jam’iyyar PDP Ba-Sanata Shehu Sani

Dan majalisar Dattawa mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa Shugaban APC na Kasa, Adams Oshiomhole, da Tsohon Gwamnan Legas, Bola Tinubu da kuma Tsohon Gwamnan Kaduna Balarabe Musa ne suka hana shi canja sheka zuwa PDP.

Ya kara da cewa wadannan mutane sun ja hankalinsa kan cewa dukkan ‘yan majalisar da suka koma PDP, dama can asali daga jam’iyyar suka fito kuma shi ba zai iya tafiyar irin wadannan ‘yan siyasar ba.
A bangare daya kuma, Gwamnan Kaduna Malam Nasir El Rufa’i ya jaddada duk da yake Sanata Shehu Sani bai koma PDP ba amma dole sai ya nemi afuwar al’ummar jihar musamman yadda ya hana Bankin duniya ya ba jihar bashin gudanar da muhimman ayyuka, ba ya ga haka ma, jam’iyyar APC ta jihar ta dakatar da shi.
#Rariya

No comments:

Post a Comment