‘Yan Jam’iyyar PDP Mutum Dubu Takwas Sun Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar APC, A Karamar Hukumar Mallammadori Dake Jihar Jigawa.
Ambasada Ahmed Abdulhamid Mallammadori, Tsohon Minista Tama Da Karafa, Shine Ya Karbe su, Inda Suka Bayyana Cewa Dama Ambasada Ahmed Abdulhamid Shine Jagoransu A Lokacin Yana PDP. Dan Haka Sun Biyo shi Zuwa Jam’iyyar APC Bayan Amincewa Da Kudire-Kudire Da Aiyukan Alkairin Da Gwamnatin APC Take Shinfidawa Al’ummar Karamar Hukumar Mallammadori.
Shugaban Jam’iyyar APC Shiyar Kasar Hadejia, Alh Abdullahi Ango, Yace Jam’iyyar APC Tayi Farin Ciki Da Wannan Babban Kamun Da Tayi, Inda Yacigaba Da Cewa Duk Mai Kishin Jihar Jigawa Bazai Ki Jam’iyyar APC Duba Da Irin Aiyukan Alkairin Da Gwamnatin Jihar Jigawa Karkashin Jagorancin Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar Take yi Al’umma.

No comments:
Post a Comment